Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 8:15-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Bayan da ka tsarkake su, ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, za su cancanta su yi aiki a alfarwa ta sujada.

16. Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra'ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato dukan 'ya'yan farin Isra'ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.

17. A ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa, na mutum, da na dabba.

18. Na kuwa keɓe wa kaina Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa.

19. Daga cikin Isra'ilawa kuwa na ba da Lawiyawa ga Haruna da 'ya'yansa maza don su yi wa Isra'ilawa hidima a alfarwa ta sujada, su kuma yi kafara dominsu don kada annoba ta sami Isra'ilawa sa'ad da suka kusaci alfarwa ta sujada.”

20. Musa da Haruna kuwa da dukan taron Isra'ilawa suka yi wa Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarce Musa, haka kuwa Isra'ilawa suka yi musu.

21. Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka wanke tufafinsu. Haruna kuwa ya keɓe su, suka zama kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji, ya kuma yi kafara dominsu don ya tsarkake su.

22. Bayan haka Lawiyawa suka shiga alfarwa ta sujada don su yi aiki a gaban Haruna da 'ya'yansa maza, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa a kan Lawiyawa, haka kuwa suka yi musu.

23. Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

24. “Wannan ita ce ka'idar aikin Lawiyawa, tun daga mai shekara ashirin da biyar zuwa gaba, zai shiga yin aiki a alfarwa ta sujada.

25. Amma daga shekara hamsin, sai su huta daga aiki alfarwa ta sujada.

Karanta cikakken babi L. Kid 8