Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 8:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa ya

2. faɗa wa Haruna cewa, “Sa'ad da za ka kakkafa fitilun nan bakwai, sai ka kakkafa su yadda za su haskaka sashin gaba.”

3. Haka kuwa Haruna ya yi. Ya kakkafa fitilun yadda za su haskaka a gaban alkukin, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

4. Da zinariya aka ƙera alkukin tun daga samansa har gindinsa, bisa ga fasalin da Ubangiji ya nuna wa Musa.

5. Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

6. “Keɓe Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa ka tsarkake su.

7. Ga yadda za ka tsarkake su. Ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa. Su aske jikunansu duka, su kuma a wanke tufafinsu, sa'an nan za su tsarkaka.

8. Su kuma ɗauki maraƙi tare da lallausan garin hadaya kwaɓaɓɓe da mai. Kai kuma ka ɗauki wani maraƙi na yin hadaya don zunubi.

9. Sa'an nan ka gabatar da Lawiyawa a gaban alfarwa ta sujada, ka kira taron Isra'ilawa duka.

10. Sa'ad da ka gabatar da Lawiyawa a gaban Ubangiji, sai Isra'ilawa su ɗibiya hannuwansu bisa Lawiyawa.

11. Haruna kuma zai gabatar da Lawiyawan a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa daga Isra'ilawa domin su zama masu yi wa Ubangiji aiki.

12. Sa'an nan Lawiyawa za su ɗibiya hannuwansu a bisa kawunan maruƙan. Za ka yi hadaya domin zunubi da maraƙi ɗaya, ɗaya kuma ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji domin ka yi kafara saboda Lawiyawa.

13. “Za ka keɓe Lawiyawa su zama kamar hadaya ta kaɗawa gare ni, ka sa Haruna da 'ya'yansa maza su lura da su.

Karanta cikakken babi L. Kid 8