Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Hadayun Keɓe Bagade

1. A ranar da Musa ya gama kafa alfarwa ta sujada, ya shafa mata mai, ya tsarkake ta, da dukan kayayyakinta, ya kuma shafa wa bagaden mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.

2. Sai shugabannin Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanninsu, su ne shugabannin kabilansu, waɗanda suka shugabanci waɗannan da aka ƙidaya,

3. suka kawo hadayarsu a gaban Ubangiji, karusai shida rufaffu, da takarkarai goma sha biyu. Shugabanni biyu suka ba da karusa ɗaya, kowannensu kuwa ya ba da takarkari ɗaya, da suka gama miƙa su,

4. sai Ubangiji ya ce wa Musa,

5. “Karɓi waɗannan daga gare su domin a yi aiki da su a alfarwa ta sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”

6. Musa kuwa ya karɓi karusan, da takarkaran, ya ba Lawiyawa.

7. Ya ba 'ya'ya maza na Gershon karusai biyu da takarkarai huɗu bisa ga aikinsu.

8. Ya kuwa ba 'ya'ya maza na Merari karusai huɗu da takarkarai takwas bisa ga aikinsu, a hannun Itamar ɗan Haruna, firist.

9. Amma bai ba 'ya'ya maza na Kohat kome ba, domin aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.

10. Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden,

11. Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Bari shugabannin su kawo hadayunsa domin keɓewar bagade, har kwana sha biyu, kowa a ranarsa.”

12-83. Suka miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka, Kabila Shugaba Yahuza Nashon ɗan Amminadab Issaka Netanel ɗan Zuwar Zabaluna Eliyab ɗan Helon Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Ashiru Fagiyel ɗan Okran Naftali Ahira ɗan Enan Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba'in, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da 'yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama.

84-88. Ga jimillar hadayun da shugabanni goma sha biyu suka kawo domin keɓewar bagaden:farantan azurfa goma sha biyu da kwanonin azurfa goma sha biyu, duka nauyinsu shekel dubu biyu da ɗari huɗucokulan zinariya goma sha biyu, nauyinsu duka shekel ɗari da ashirin cike da kayan ƙanshibijimai goma sha biyu, da raguna goma sha biyu, da 'yan raguna goma sha biyu bana ɗaya ɗaya, da kuma hadaya ta gari da za a haɗa da waɗannan domin hadaya ta ƙonawaawaki goma sha biyu domin hadaya don zunubibijimai ashirin da huɗu, da raguna sittin, da awaki sittin, da 'yan raguna bana ɗaya ɗaya guda sittin domin hadaya ta salama.

89. Duk lokacin da Musa ya shiga alfarwa ta sujada domin ya yi magana da Ubangiji, sai ya ji Ubangiji yana magana da shi daga bisa murfin akwatin alkawari, a tsakanin kerubobi masu fikafikai biyu.