Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 5:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

2. “Ka umarci Isra'ilawa su fitar da kuturu, da mai ɗiga, da wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin zango.

3. Su fitar da mace ko namiji daga cikin zango, don kada su ƙazantar da zangonku inda nake zaune.”

4. Sai Isra'ilawa suka fitar da su daga cikin zango kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Haka mutanen Isra'ila suka yi.

5. Ubangiji kuma ya ba Musa

6. waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa. Idan wani ya aikata rashin gaskiya ga Ubangiji, ta wurin saɓa wa wani,

7. sai ya hurta zunubinsa, sa'an nan ya biya cikakkiyar diyyar abin da ƙarin humushin abin, ya ba mutumin da ya yi wa laifin.

8. Idan wanda ya yi wa laifin ya rasu, ba shi kuma da wani dangi na kusa wanda za a ba diyyar, sai a kai diyyar gaban Ubangiji domin firist, tare da ragon hadaya, don yin kafarar da za a yi masa.

9. Dukan sadakoki na tsarkakakkun abubuwa na Isra'ilawa waɗanda sukan kawo wa firist, za su zama nasa.

Karanta cikakken babi L. Kid 5