Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 36:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ba za a sāke gādon Isra'ilawa daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowane mutum na cikin jama'ar Isra'ila zai riƙe gādonsa na kabilar kakanninsa.

8. Kowace 'ya mace wadda ta ci gādo a wata kabilar Isra'ila, sai ta yi aure a cikin kabilar kakanta domin kowane Ba'isra'ile ya ci gādon kakanninsa.

9. Ta yin haka ba za a sāke gādo daga wata kabila zuwa wata ba, gama kowace kabilar Isra'ila za ta riƙe gādonta.’ ”

10. Sai 'ya'yan Zelofehad mata, wato Mala, da Tirza, da Hogla, da Milka, da Nowa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

11. Suka auri 'ya'yan 'yan'uwan mahaifinsu.

12. Sun yi aure a cikin iyalan 'ya'yan Manassa, ɗan Yusufu. Gādonsu kuwa bai ɓalle daga cikin kabilar iyalin kakansu ba.

13. Waɗannan su ne umarnai da ka'idodi waɗanda Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila ta wurin Musa a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko.

Karanta cikakken babi L. Kid 36