Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 34:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sa'an nan za ta gangara daga Shefam zuwa Ribla wajen gabashin Ayin. Za ta kuma gangara har ta kai Tekun Galili a wajen gabas.

12. Iyakar kuma za ta gangara har zuwa Urdun, ta tsaya a Tekun Gishiri. Wannan ita ce ƙasarsu da iyakokinta kewaye da ita.

13. Sai Musa ya ce wa Isra'ilawa, “Wannan ita ce ƙasar da za ku gāda ta hanyar jefa kuri'a. Ƙasar da Ubangiji ya umarta a ba kabilai tara da rabi.

14. Gama kabilar Ra'ubainu da ta Gad da kuma rabin kabilar Manassa sun riga sun karɓi nasu gādo.

15. Kabilan nan biyu da rabi sun karɓi nasu gādo a wancan hayin Urdun a gabashin Yariko.”

16. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

17. “Ga sunayen mutanen da za su taimake ka raba gādon ƙasar, Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun.

18. Za ka kuma ɗauki shugaba ɗaya daga kowace kabila don su raba gādon ƙasar.

19. Waɗannan su ne sunayen mutanen, Kalibu ɗan Yefunne daga kabilar Yahuza.

20. Shemuyel ɗan Ammihud daga kabilar Saminu.

21. Elidad ɗan Kislon daga kabilar Biliyaminu.

Karanta cikakken babi L. Kid 34