Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 33:32-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Suka tashi daga Bene-ya'akan suka sauka a Hor-hagidgad.

33. Da suka tashi daga Hor-hagidgad suka sauka a Yotbata.

34. Suka kama hanya daga Yotbata suka sauka a Abrona.

35. Da suka tashi daga Abrona, sai suka sauka a Eziyon-geber.

36. Suka tashi daga Eziyon-geber suka sauka a jejin Zin, wato Kadesh.

37. Da suka kama hanya daga Kadesh suka sauka a Dutsen Hor a kan iyakar ƙasar Edom.

38. Bisa ga umarnin Ubangiji, Haruna firist ya hau Dutsen Hor inda ya rasu a rana ta fari ga watan biyar a shekara ta arba'in ta fitowar jama'ar Isra'ila daga ƙasar Masar.

39. Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku sa'ad da ya rasu a Dutsen Hor.

40. Sai Sarkin Arad, Bakan'ane wanda yake zaune a Negeb, a ƙasar Kan'ana, ya ji zuwan Isra'ilawa.

41. Isra'ilawa kuma suka tashi daga Dutsen Hor, suka sauka a Zalmona.

42. Daga Zalamona suka sauka a Funon.

43. Da suka tashi daga Funon, sai suka sauka a Obot.

Karanta cikakken babi L. Kid 33