21. Da suka tashi daga Libna, sai suka sauka a Rissa.
22. Da suka tashi daga Rissa, suka sauka a Kehelata.
23. Suka tashi daga Kehelata suka sauka a Dutsen Shifer.
24. Suka tashi daga Dutsen Shifer suka sauka a Harada.
25. Da suka tashi daga Harada, suka sauka a Makelot.
26. Suka tashi daga Makelot suka sauka a Tahat.
27. Suka tashi daga Tahat suka sauka a Tara.
28. Suka kama hanya daga Tara suka sauka a Mitka.
29. Suka kuma kama hanya daga Mitka suka sauka a Hashmona.
30. Daga Hashmona suka sauka a Moserot.
31. Da suka tashi daga Moserot suka sauka a Bene-ya'akan.