11. Da suka tashi daga Bahar Maliya suka sauka a jejin Sin.
12. Suka tashi daga jejin Sin, suka sauka a Dofka.
13. Daga Dofka suka tafi Alush.
14. Suka tashi daga Alush suka sauka a Refidim inda mutane suka rasa ruwan sha.
15. Suka tashi daga Refidim suka sauka a jejin Sinai.
16. Da suka tashi daga jejin Sinai, sai suka sauka a Kibrot-hata'awa.