Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 33:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan su ne wuraren da Isra'ilawa suka yi zango sa'ad da suka fita runduna runduna daga ƙasar Masar ta hannun Musa da Haruna.

2. Bisa ga faɗar Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tashinsu da wuraren saukarsu. Wuraren saukarsu da na tashinsu ke nan.

3. Sun tashi daga Ramases a rana ta goma sha biyar ga watan fari. A kashegarin Idin Ƙetarewa ne suka fita gabagaɗi a gaban dukan Masarawa.

4. Masarawa suna ta binne gawawwakin 'ya'yan farinsu da Ubangiji ya karkashe musu. Banda 'ya'yan farinsu kuma Ubangiji ya hukunta wa allolinsu.

5. Isra'ilawa kuwa suka tashi daga Ramases suka sauka a Sukkot.

6. Suka tashi daga Sukkot suka sauka a Etam wadda take a gefen jejin.

7. Da suka tashi daga Etam, sai suka juya zuwa Fi-hahirot wadda take gaban Ba'al-zefon suka sauka a gaban Migdol.

8. Da suka tashi daga gaban Fi-hahirot sai suka haye teku zuwa cikin jejin. Suka yi tafiya kwana uku a jejin Etam, suka sauka a Mara.

9. Suka tashi daga Mara suka zo Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa guda goma sha biyu da itacen dabino guda saba'in. Sai suka sauka a can.

10. Suka tashi daga Elim, suka sauka a gefen Bahar Maliya.

Karanta cikakken babi L. Kid 33