Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 32:20-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sai Musa ya ce musu, “Idan za ku yi haka, wato ku ɗauki makamai, ku tafi yaƙi a gaban Ubangiji,

21. kowane sojanku ya haye Urdun a gaban Ubangiji, har lokacin da Ubangiji ya kori abokan gābansa daga gabansa,

22. har kuma lokacin da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji kafin ku koma, to, za ku kuɓuta daga alhakinku a gaban Ubangiji da jama'ar Isra'ila. Wannan ƙasa kuwa za ta zama mallakarku a gaban Ubangiji.

23. Idan kuwa ba ku yi haka ba, kun yi wa Ubangiji laifi, ku tabbata fa alhakin zunubinku zai kama ku.

24. To, sai ku gina wa 'ya'yanku birane, ku gina wa garkunanku garu, amma ku aikata abin da kuka faɗa da bakinku.”

25. Sai Gadawa da Ra'ubainawa suka amsa wa Musa, suka ce, “Barorinka za su yi kamar yadda ka umarta.

26. 'Ya'yanmu, da matanmu, da tumakinmu, da shanunmu za su zauna a birane a nan Gileyad.

27. Amma kowane soja a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji zuwa yaƙi kamar yadda shugabanmu ya faɗa.”

28. Sai Musa ya yi wa Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra'ila kashedi a kansu,

29. ya ce, “Idan kowane soja na Gadawa da Ra'ubainawa zai haye Urdun tare da ku don yaƙi har an ci ƙasar dominku, to, sai ku ba su ƙasar Gileyad ta zama mallakarsu.

30. Amma idan ba su haye tare da ku da shirin yaƙi ba, to, sai ku ba su gādo tare da ku a cikin ƙasar Kan'aniyawa.”

31. Gadawa da Ra'ubainawa kuwa suka ce, “Kamar yadda Ubangiji ya ce wa barorinka, haka za mu yi.

32. Za mu haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa cikin ƙasar Kan'aniyawa, amma za mu sami gādonmu a wannan hayin Urdun.”

33. Sa'an nan Musa ya ba Gadawa, da Ra'ubainawa, da rabin mutanen Manassa, ɗan Yusufu, mulkin Sihon, Sarkin Amoriyawa, da mulkin Og, Sarkin Bashan, wato ƙasar da biranenta da karkaransu.

34. Sai Gadawa suka gina Dibon, da Atarot, da Arower,

Karanta cikakken babi L. Kid 32