Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 32:19-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Gama ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayi na gabashin Urdun.”

20. Sai Musa ya ce musu, “Idan za ku yi haka, wato ku ɗauki makamai, ku tafi yaƙi a gaban Ubangiji,

21. kowane sojanku ya haye Urdun a gaban Ubangiji, har lokacin da Ubangiji ya kori abokan gābansa daga gabansa,

22. har kuma lokacin da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji kafin ku koma, to, za ku kuɓuta daga alhakinku a gaban Ubangiji da jama'ar Isra'ila. Wannan ƙasa kuwa za ta zama mallakarku a gaban Ubangiji.

23. Idan kuwa ba ku yi haka ba, kun yi wa Ubangiji laifi, ku tabbata fa alhakin zunubinku zai kama ku.

24. To, sai ku gina wa 'ya'yanku birane, ku gina wa garkunanku garu, amma ku aikata abin da kuka faɗa da bakinku.”

25. Sai Gadawa da Ra'ubainawa suka amsa wa Musa, suka ce, “Barorinka za su yi kamar yadda ka umarta.

26. 'Ya'yanmu, da matanmu, da tumakinmu, da shanunmu za su zauna a birane a nan Gileyad.

27. Amma kowane soja a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji zuwa yaƙi kamar yadda shugabanmu ya faɗa.”

28. Sai Musa ya yi wa Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra'ila kashedi a kansu,

29. ya ce, “Idan kowane soja na Gadawa da Ra'ubainawa zai haye Urdun tare da ku don yaƙi har an ci ƙasar dominku, to, sai ku ba su ƙasar Gileyad ta zama mallakarsu.

Karanta cikakken babi L. Kid 32