Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 32:14-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ga shi, ku kuma da kuke 'ya'yan mugayen mutanen nan, ku da kuke a matsayin iyayenku, kuna so ku ƙara sa Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.

15. Gama idan kun ƙi binsa, zai sāke yashe ku a jeji. Ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakar mutanen nan duka.”

16. Sai suka zo kusa da shi, suka ce, “Za mu gina garu na dutse don mu kāre dabbobinmu, da birane don 'ya'yanmu a nan.

17. 'Ya'yanmu za su zauna a biranen don gudun mazaunan ƙasar, amma mu za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra'ilawa, har mu kai su wuraren zamansu.

18. Ba kuwa za mu koma gidajenmu ba, sai lokacin da kowane Ba'isra'ile ya sami gādonsa.

19. Gama ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayi na gabashin Urdun.”

20. Sai Musa ya ce musu, “Idan za ku yi haka, wato ku ɗauki makamai, ku tafi yaƙi a gaban Ubangiji,

21. kowane sojanku ya haye Urdun a gaban Ubangiji, har lokacin da Ubangiji ya kori abokan gābansa daga gabansa,

22. har kuma lokacin da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji kafin ku koma, to, za ku kuɓuta daga alhakinku a gaban Ubangiji da jama'ar Isra'ila. Wannan ƙasa kuwa za ta zama mallakarku a gaban Ubangiji.

23. Idan kuwa ba ku yi haka ba, kun yi wa Ubangiji laifi, ku tabbata fa alhakin zunubinku zai kama ku.

24. To, sai ku gina wa 'ya'yanku birane, ku gina wa garkunanku garu, amma ku aikata abin da kuka faɗa da bakinku.”

25. Sai Gadawa da Ra'ubainawa suka amsa wa Musa, suka ce, “Barorinka za su yi kamar yadda ka umarta.

26. 'Ya'yanmu, da matanmu, da tumakinmu, da shanunmu za su zauna a birane a nan Gileyad.

27. Amma kowane soja a cikinmu zai haye a gaban Ubangiji zuwa yaƙi kamar yadda shugabanmu ya faɗa.”

Karanta cikakken babi L. Kid 32