Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 31:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa,

2. “Ka ɗaukar wa Isra'ilawa fansa a kan Madayanawa. Bayan ka yi wannan za ka mutu.”

3. Musa kuwa ya ce wa jama'a, “Ku sa mazajen da suke cikinku su yi shiri, su yi ɗamarar yaƙi, don su tafi su yi yaƙi da Madayanawa, su ɗaukar wa ubangiji fansa a kansu.

4. Sai ku aiki mutum dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila zuwa wurin yaƙi.”

5. Aka samo mutum dubu goma sha biyu (12,000) shiryayyu don yaƙi, daga cikin dubban Isra'ilawa, mutum dubu ɗaya daga kowace kabila.

6. Musa ya aike su zuwa yaƙi tare da Finehas, ɗan Ele'azara firist, da akwatin alkawari, da ƙahonin kiran yaƙi a hannun Finehas.

7. Suka yi yaƙi da Madayanawa suka kashe musu kowane namiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

8. Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal'amu ɗan Beyor.

9. Isra'ilawa suka kwashi mata da yaran Madayanawa bayi. Suka washe shanunsu, da tumakinsu da dukan dukiyarsu ganima.

10. Suka kuma ƙone dukan biranen zamansu da dukan san saninsu da wuta.

Karanta cikakken babi L. Kid 31