Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 30:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Idan kuwa ta yi aure lokacin da take da wa'adi ko kuwa rantsuwar da ta yi da garaje,

7. idan mijinta ya ji wa'adin ko rantsuwar amma bai ce mata kome ba a ranar da ya ji, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su tabbata.

8. Amma idan mijinta bai goyi bayanta a ranar da ya ji ba, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su warware, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.

9. Mace wadda mijinta ya rasu ko sakakkiya, dole ta cika wa'adin da ta yi, da kowane alkawari, za su tabbata.

10. Idan macen aure ta yi wa'adi ko alkawari ba za ta yi wani abu ba,

11. idan mijinta ya ji, amma bai ce mata kome ba, to, sai wa'adinta da kowace irin rantsuwarta su tabbata.

12. Amma idan mijinta ya hana ta a ranar da ya ji, to, sai ta bari. Mijinta ya hana ta É—aukar wa'adin, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.

Karanta cikakken babi L. Kid 30