Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 30:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. idan mahaifinta ya ji wa'adinta da rantsuwarta wadda ta ɗaure kanta da su, bai ce mata kome ba, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su tabbata.

5. Amma idan mahaifinta ya ji, ya nuna rashin yarda, to, wa'adinta da rantsuwarta ba za su tsaya ba, Ubangiji kuwa zai gafarce ta domin mahaifinta bai yardar mata ba.

6. Idan kuwa ta yi aure lokacin da take da wa'adi ko kuwa rantsuwar da ta yi da garaje,

7. idan mijinta ya ji wa'adin ko rantsuwar amma bai ce mata kome ba a ranar da ya ji, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su tabbata.

8. Amma idan mijinta bai goyi bayanta a ranar da ya ji ba, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su warware, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.

9. Mace wadda mijinta ya rasu ko sakakkiya, dole ta cika wa'adin da ta yi, da kowane alkawari, za su tabbata.

Karanta cikakken babi L. Kid 30