Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 28:25-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. A rana ta bakwai za a yi tsattsarkan taro, ba za a yi aiki ba.

26. Za a yi tsattsarkan taro a ranar nunan fari, wato idi na mako bakwai lokacin da za a miƙa wa Ubangiji hadaya da sabon hatsi. A ranar ba za a yi aiki ba.

27. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

28. Za a miƙa hadaya ta gāri tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da mai, gari humushi uku na garwa, za a miƙa tare da kowane bijimi, humushi biyu na garwa don rago,

29. da humushin garwa don kowane ɗan rago.

30. Za a miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi, domin a yi kafara.

31. Banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, sai a miƙa waɗannan tare da hadayarsu ta sha. Dabbobin su zama marasa lahani.

Karanta cikakken babi L. Kid 28