Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 27:18-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Joshuwa, ɗan Nun, mutumin da ya dace, ka ɗibiya masa hannuwanka,

19. ka sa shi ya tsaya a gaban Ele'azara, firist, da gaban dukan taron, sa'an nan ka keɓe shi a gabansu.

20. Ka danƙa masa ikonka don taron jama'ar Isra'ila su yi masa biyayya.

21. Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.”

22. Musa kuwa ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki Joshuwa, ya sa shi ya tsaya a gaban Ele'azara, firist, da gaban dukan taron.

23. Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya keɓe shi kamar yadda Ubangiji ya umarta.

Karanta cikakken babi L. Kid 27