Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 26:47-60 Littafi Mai Tsarki (HAU)

47. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ashiru. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da uku da ɗari huɗu (53,400).

48. Kabilar Naftali ke nan bisa ga iyalansu, Yezeyel, da Guni,

49. da Yezer, da Shallum.

50. Waɗannan su ne iyalan kabilar Naftali. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari huɗu (45,400).

51. Jimillar Isra'ilawa maza waɗanda aka ƙidaya, dubu ɗari shida da dubu ɗaya da ɗari bakwai da talatin (601,730).

52. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

53. “A raba wa waɗannan mutane gādon ƙasar bisa ga yawan kowace kabila.

54. Za ka ba babbar kabila babban rabo, ka ba ƙaramar kabila ƙaramin rabo. Kowace kabila za a ba ta gādo bisa ga yawanta.

55. Amma za a rarraba musu gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar kuri'a.

56. Za a rarraba gādo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri'a.”

57. Waɗannan su ne Lawiyawan da aka ƙidaya bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari.

58. Sauran iyalin Lawiyawa daga zuriyar Libni ne, da Hebron, da Mali, da Mushi, da Kora. Kohat shi ne mahaifin Amram,

59. wanda ya auri Yokabed 'yar Lawi wadda aka haifa masa a Masar. Yokabed ta haifa wa Amram, Haruna, da Musa, da Maryamu, 'yar'uwarsu.

60. Haruna yana da 'ya'ya huɗu maza, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.

Karanta cikakken babi L. Kid 26