Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 26:41-55 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. Waɗannan su ne 'ya'yan Biliyaminu bisa ga iyalansu. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari shida (45,600).

42. Waɗannan su ne kabilar Dan bisa ga iyalansu, Hushim. Waɗannan su ne iyalan kabilar Dan.

43. Yawansu ya kai dubu sittin da huɗu da ɗari huɗu (64,400).

44. Kabilar Ashiru ke nan bisa ga iyalansu, Yimna, da Yishwi, da Beriya.

45. Iyalin Beriya kuwa sune Eber, da Malkiyel, suna lasafta kansu a zuriyar Beriya.

46. Sunan 'yar Ashiru Sera.

47. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ashiru. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da uku da ɗari huɗu (53,400).

48. Kabilar Naftali ke nan bisa ga iyalansu, Yezeyel, da Guni,

49. da Yezer, da Shallum.

50. Waɗannan su ne iyalan kabilar Naftali. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari huɗu (45,400).

51. Jimillar Isra'ilawa maza waɗanda aka ƙidaya, dubu ɗari shida da dubu ɗaya da ɗari bakwai da talatin (601,730).

52. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

53. “A raba wa waɗannan mutane gādon ƙasar bisa ga yawan kowace kabila.

54. Za ka ba babbar kabila babban rabo, ka ba ƙaramar kabila ƙaramin rabo. Kowace kabila za a ba ta gādo bisa ga yawanta.

55. Amma za a rarraba musu gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar kuri'a.

Karanta cikakken babi L. Kid 26