Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 26:27-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Waɗannan su ne iyalan kabilar Zabaluna. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da ɗari biyar (60,500).

28. Kabilar Yusufu ke nan bisa ga iyalansu, wato Manassa da Ifraimu.

29. Kabilar Manassa, su ne Makir ɗan Manassa. Makir ya haifi Gileyad wanda ya zama tushen zuriyar Gileyad.

30. 'Ya'yan Gileyad, maza su ne Abiyezer, da Helek,

31. da Asriyel, da Shekem,

32. da Shemida, da Hefer.

33. Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

34. Waɗannan su ne iyalan kabilar Manassa. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da biyu da ɗari bakwai (52,700).

35. Waɗannan su ne kabilar Ifraimu bisa ga iyalansu, Shutela, da Beker, da Tahat.

Karanta cikakken babi L. Kid 26