Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 26:22-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Waɗannan su ne iyalan kabilar Yahuza. Yawan mutanensu ya kai dubu saba'in da shida da ɗari biyar (76,500).

23. Kabilar Issaka ke nan bisa ga iyalansu, da Tola, da Fuwa,

24. da Yashub, da Shimron.

25. Waɗannan su ne iyalan kabilar Issaka. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da huɗu da ɗari uku (64,300).

26. Kabilar Zabaluna ke nan bisa ga iyalansu, Sered, da Elon, da Yaleyel.

27. Waɗannan su ne iyalan kabilar Zabaluna. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da ɗari biyar (60,500).

28. Kabilar Yusufu ke nan bisa ga iyalansu, wato Manassa da Ifraimu.

29. Kabilar Manassa, su ne Makir ɗan Manassa. Makir ya haifi Gileyad wanda ya zama tushen zuriyar Gileyad.

30. 'Ya'yan Gileyad, maza su ne Abiyezer, da Helek,

31. da Asriyel, da Shekem,

32. da Shemida, da Hefer.

33. Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

Karanta cikakken babi L. Kid 26