Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 26:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan annobar, sai Ubangiji ya ce wa Musa da Ele'azara, ɗan Haruna, firist,

2. “Ku ƙidaya dukan taron jama'ar Isra'ila tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba bisa ga gidajen ubanninsu. Ku ƙidaya duk wanda ya isa zuwa yaƙi a cikin Isra'ilawa.”

3. Sai Musa da Ele'azara, firist, suka yi musu magana a filayen Mowab daura da Yariko, suka ce,

4. “A ƙidaya mutane tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba kamar yadda Ubangiji ya umarta.”Isra'ilawa waɗanda suka fita daga ƙasar Masar ke nan.

5. Ra'ubainu shi ne ɗan fari na Yakubu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, su ne Hanok, da Fallu,

6. da Hesruna, da Karmi.

7. Waɗannan yawansu ya kai dubu arba'in da uku da ɗari bakwai da talatin (43,730).

8. Fallu ya haifi Eliyab.

9. 'Ya'yan Eliyab, maza su ne Yemuwel, da Datan, da Abiram. Datan da Abiram ne aka zaɓa daga cikin taron jama'ar, suna cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Musa da Haruna, har ma da Ubangiji.

10. Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora. Wuta kuma ta cinye sauran mutanen ƙungiyar, mutum ɗari biyu da hamsin suka mutu. Suka zama abin faɗakarwa.

11. Amma 'ya'yan Kora ba su mutu ba.

12. 'Ya'yan Saminu, maza, bisa ga iyalansu, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin,

13. da Zohar, da Shawul. Waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu.

Karanta cikakken babi L. Kid 26