Jama'a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama'ar.