Da Sarkin Arad, Bakan'ane, wanda yake zaune a Negeb, ya ji Isra'ilawa suna zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fita ya yi yaƙi da Isra'ilawa, ya kama waɗansu daga cikinsu.