Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 20:16-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sa'ad da muka yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya aiko mala'ikansa, ya fisshe mu daga Masar. Ga mu nan a Kadesh, garin da yake kan iyakar ƙasarka.

17. Ka yarda mana mu ratsa ƙasarka, ba za mu bi ta cikin gona, ko gonar inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba. Mu dai za mu bi gwadaben sarki, ba za mu kauce dama ko hagu ba, har mu wuce ƙasarka.”

18. Amma Edomawa suka ce masa, “Ba za ku ratsa ta ƙasarmu ba! Idan kuwa kun ce za ku gwada, za mu fita mu ci ku da yaƙi.”

19. Amma mutanen Isra'ila suka amsa musu suka ce, “Ai, za mu bi gwadabe ne kawai, idan kuwa mu da dabbobinmu mun sha ruwanku, sai mu biya, mu dai, a yardar mana mu wuce kawai.”

20. Amma Edomawa suka sāke cewa, “Ba mu yarda ba.” Sai suka fito da runduna mai yawa su yi yaƙi da su.

21. Da haka Edomawa suka hana Isra'ilawa ratsa ƙasarsu. Sai Isra'ilawa suka kauce musu.

22-23. Sai taron jama'ar Isra'ila suka kama tafiya daga Kadesh, suka je Dutsen Hor, a kan iyakar ƙasar Edom. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna a can,

24. “Haruna ba zai shiga ƙasar da na alkawarta zan ba Isra'ila ba, zai mutu, gama ku biyun nan kuka tayar wa umarnina a Meriba.

25. Ka kawo Haruna da ɗansa, Ele'azara, bisa Dutsen Hor.

26. Ka tuɓe wa Haruna rigunansa na firist, ka sa wa ɗansa, Ele'azara. Haruna zai mutu can.”

27. Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau bisa Dutsen Hor a idon dukan taron jama'a.

28. Sai Musa ya tuɓe wa Haruna rigunansa na firist ya sa wa Ele'azara ɗan Haruna. Haruna kuwa ya rasu a kan dutsen. Sa'an nan Musa da Ele'azara suka sauko daga kan dutsen.

29. Sa'ad da dukan jama'a suka ga Haruna ya rasu, sai duka suka yi makoki dominsa har kwana talatin.

Karanta cikakken babi L. Kid 20