Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 17:8-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Kashegari Musa ya shiga alfarwar, sai ga shi, sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya huda, ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi 'ya'yan almon nunannu, wato wani irin itace ne mai kama da na yazawa.

9. Musa kuwa ya fito wa Isra'ilawa da dukan sandunan da aka ajiye a gaban Ubangiji. Suka duba, kowanne ya É—auki sandansa.

10. Ubangiji ya ce wa Musa, “Mayar da sandan Haruna a akwatin alkawari, alama ce ga masu tawaye ta cewa za su mutu idan ba su daina gunaguninsu ba.”

11. Haka kuwa Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi.

12. Isra'ilawa suka ce wa Musa, “Ba shakka, mun hallaka. Mun lalace, dukanmu mun lalace.

13. Duk wanda ya kusaci alfarwa ta sujada ta Ubangiji, zai mutu. Ashe, dukanmu za mu mutu ke nan!”

Karanta cikakken babi L. Kid 17