Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 15:31-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. gama ya raina maganar Ubangiji, ya karya umarninsa. Hakika za a kashe mutumin nan, alhakin zunubinsa, yana wuyansa.

32. Sa'ad da Isra'ilawa suke jeji, sai aka iske wani yana tattara itace a ranar Asabar.

33. Sai suka kai shi wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'a.

34. Aka sa shi a gidan waƙafi domin ba a bayyana abin da za a yi da shi ba tukuna.

35. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “A kashe mutumin, dukan taron jama'a za su jajjefe shi da duwatsu a bayan zangon.”

36. Dukan taron jama'a suka kai shi bayan zangon, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

37. Ubangiji ya umarci Musa ya ce,

38. “Ka faɗa wa Isra'ilawa su yi wa shafin rigunansu tuntaye a dukan zamananku. A kan kowane tuntu, su sa shuɗin zare.

39. Tuntu zai zama musu abin dubawa don su riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji su aikata su, don kada su bi son zuciyarsu, da sha'awar idanunsu yadda suka taɓa yi.

40. Da haka za su riƙa tunawa, su aikata dukan umarnaina su zama tsarkakakku gare ni.

41. Gama ni ne Ubangiji Allahnku, na fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Karanta cikakken babi L. Kid 15