Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 14:41-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. Amma Musa ya ce, “Me ya sa kuke karya umarnin Ubangiji? Yin haka ba zai kawo nasara ba.

42. Kada ku haura domin kada ku sha ɗibga a gaban maƙiyanku, gama Ubangiji ba ya tare da ku.

43. Gama akwai Amalekawa da Kan'aniyawa a gabanku, za su kashe ku da takobi domin kun bar bin Ubangiji, don haka Ubangiji ba zai kasance tare da ku ba.”

44. Amma sai suka yi izgili, suka haura kan tudun, amma akwatin alkawari da Musa ba su bar zangon ba.

45. Sai Amalekawa da Kan'aniyawa, mazauna a kan tudun, suka gangaro, suka ci su, suka runtume su har Harma, wato hallakarwa.

Karanta cikakken babi L. Kid 14