Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 13:2-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Ka aiki mutane su leƙi asirin ƙasar Kan'ana wadda nake ba Isra'ilawa. Daga kowace kabila na kakanninsu, ka zaɓi mutum guda wanda yake shugaba a cikinsu.”

3-15. Musa kuwa ya yi biyayya, daga jejin Faran ya aika da waɗannan shugabanni,Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ra'ubainu.Shafat ɗan Hori, daga kabilar Saminu.Kalibu ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuza.Igal ɗan Yusufu, daga kabilar Issaka.Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Ifraimu.Falti ɗan Rafu, daga kabilar Biliyaminu.Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zabaluna.Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manassa.Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan.Setur ɗan Maikel, daga kabilar Ashiru.Nabi ɗan Wofsi,daga kabilar Naftali.Geyuwel ɗan Maci,daga kabilar Gad.

16. Waɗannan su ne mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar. Amma Musa ya ba Hosheya, ɗan Nun, suna Joshuwa.

17. Sa'ad da Musa ya aike su leƙen asirin ƙasar Kan'ana, ya ce musu, “Ku haura, ku bi ta Negeb har zuwa ƙasar tuddai,

18. ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanenta ƙarfafa ne, ko raunana ne, ko su kima ne, ko kuwa suna da yawa,

19. ko ƙasa tasu mai ni'ima ce, ko babu, ko biranensu marasa garu ne, ko masu garu ne,

20. ko ƙasar tana da wadata,ko matalauciya ce, ko ƙasar kurmi ce, ko fili. Ku yi jaruntaka, ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Gama lokacin farkon nunan inabi ne.)

21. Sai suka haura, suka leƙo asirin ƙasar tun daga jejin Zin har zuwa Rehob kusa da Hamat.

22. Suka haura ta wajen Negeb, suka isa Hebron inda Ahimaniyawa, da Sheshaiyawa, da Talmaiyawa, zuriyar ƙarfafan mutanen da ake kira Anakawa suke zaune. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)

Karanta cikakken babi L. Kid 13