Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 13:17-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Sa'ad da Musa ya aike su leƙen asirin ƙasar Kan'ana, ya ce musu, “Ku haura, ku bi ta Negeb har zuwa ƙasar tuddai,

18. ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanenta ƙarfafa ne, ko raunana ne, ko su kima ne, ko kuwa suna da yawa,

19. ko ƙasa tasu mai ni'ima ce, ko babu, ko biranensu marasa garu ne, ko masu garu ne,

20. ko ƙasar tana da wadata,ko matalauciya ce, ko ƙasar kurmi ce, ko fili. Ku yi jaruntaka, ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Gama lokacin farkon nunan inabi ne.)

21. Sai suka haura, suka leƙo asirin ƙasar tun daga jejin Zin har zuwa Rehob kusa da Hamat.

22. Suka haura ta wajen Negeb, suka isa Hebron inda Ahimaniyawa, da Sheshaiyawa, da Talmaiyawa, zuriyar ƙarfafan mutanen da ake kira Anakawa suke zaune. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)

23. Da suka isa Kwarin Eshkol, sai suka datse reshe guda na nonon inabi da 'ya'ya cunkus. Suka rataya a sanda, mutum biyu suka ɗauka a kafaɗunsu. Suka kuma kawo rumman da ɓaure.

24. Aka kira wurin Kwarin Eshkol, wato “nonon inabi,” saboda nonon inabi wanda 'yan leƙen ƙasa suka yanko a wurin.

25. Bayan sun yi kwana arba'in suna leƙen asirin ƙasar, sai suka komo.

26. Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'ar Isra'ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo.

27. Suka ce wa Musa, “Mun tafi ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana da yalwar abinci, ga kuma amfanin ƙasar.

28. Amma mazaunan ƙasar ƙarfafa ne, biranenta kuma manya ne, masu garu, banda wannan kuma, mun ga Anakawa a can.

29. Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”

Karanta cikakken babi L. Kid 13