Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 8:15-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai Musa ya yanka shi, ya ɗibi jinin a yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye, ya tsarkake bagaden, ya zuba jinin a gindin bagaden, ya keɓe shi don ya yi kafara dominsa.

16. Sai ya ɗauki dukan kitsen da yake bisa kayan ciki da matsarmama, da ƙodoji biyu da kitsensu, ya ƙone su bisa bagaden.

17. Amma ya ƙone naman bijimin da fatarsa da tarosonsa a bayan zangon kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

18. Sa'an nan ya kawo rago na yin hadaya ta ƙonawa. Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.

19. Sai ya yanka ragon, ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa.

20. Da aka yanyanka ragon gunduwa gunduwa, sai Musa ya ƙone kan, da gunduwoyin, da kitsen.

21. Sa'ad da kuma aka wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sai ya ƙone ragon duka a bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

22. Musa ya kawo ɗayan ragon keɓewa, sai Haruna da 'ya'yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan kan ragon.

23. Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama.

24. Sai aka kawo 'ya'yan Haruna, maza, Musa kuma ya sa jinin a leɓatun kunnensu na dama, da manyan yatsotsi na hannuwansu na dama, da manyan yatsotsin ƙafafu na dama. Sa'an nan ya yayyafa jinin kewaye da bagaden.

25. Ya kuma ɗauki kitsen, da wutsiya mai kitse, da dukan kitsen da yake bisa kayan ciki, da matsarmama da ƙodoji biyu da kitsensu, da cinyar dama.

26. Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, ya ɗauki waina guda marar yisti, da waina guda da aka yi da mai, da ƙosai guda. Sai ya ɗibiya su a bisa kitsen da cinyar dama.

27. Ya sa waɗannan abubuwa duka a tafin hannuwan Haruna da na 'ya'yansa maza, ya miƙa abubuwan nan domin hadayar kaɗawa ga Ubangiji.

Karanta cikakken babi L. Fir 8