Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 7:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Kowane namiji a cikin firistoci zai iya ci. Sai a wuri mai tsarki za a ci, gama tsattsarkan abu ne.

7. Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ka'idar yinsu iri ɗaya ce. Firist wanda ya yi kafarar, zai ɗauki abin da ya ragu.

8. Firist kuma wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ta wani mutum, zai ɗauki fatar abin da aka yi hadayar da shi.

9. Kowace hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, da duk wadda aka yi a tukunya ko a kaskon tuya, za su zama na firist wanda ya miƙa hadaya.

10. Kowace hadaya ta gari kuma wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, za ta zama rabon 'ya'yan Haruna, maza duka, kowa da kowa.

11. Waɗannan su ne ka'idodin hadaya ta salama wadda za a miƙa wa Ubangiji.

12. Idan domin godiya mutum ya miƙa hadaya, sai ya miƙa ta tare da abinci marar yisti, wadda aka kwaɓa da mai, da wadda aka shafa wa mai, da kuma ƙosai.

13. Tare da hadayarsa ta salama don godiya, sai ya kawo dunƙulen abincin da aka sa masa yisti.

14. Daga cikin wannan zai miƙa waina ɗaya daga kowace hadaya don hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist wanda ya yayyafa jinin hadaya ta salama.

15. Za a ci naman hadayarsa ta salama da aka miƙa don godiya a ranar da aka miƙa ta. Kada a bar naman ya kai safe.

16. Amma idan hadayarsa ta cika wa'adi ce, ko ta yardar rai ce, sai a ci ta a ranar da aka miƙa ta, kashegari kuma a ci abin da ya ragu.

17. Amma idan ba a cinye naman hadayar ba har ya kai kwana uku, kada a ci, sai a ƙone shi da wuta.

Karanta cikakken babi L. Fir 7