Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 7:27-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Duk mutumin da ya karya wannan doka za a raba shi da mutanensa.

28. Ubangiji kuma ya ba Musa waɗannan ka'idodi

29. don mutanen Isra'ila, cewa, wanda zai miƙa hadayarsa ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama.

30. Sai shi kansa ya kawo hadayar da za a ƙona. Zai kawo kitsen da ƙirjin. Za a yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin a gaban Ubangiji.

31. Firist zai ƙone kitsen a bisa bagaden, amma ƙirjin zai zama rabon Haruna da 'ya'yansa maza.

32. Za a ba firist cinya ta dama, don hadaya ta ɗagawa daga cikin hadayu na salama.

33. Cinyar ƙafar dama za ta zama rabon ɗan Haruna wanda ya miƙa jinin da kitsen hadaya ta salama.

34. Gama Ubangiji ya ba Haruna da 'ya'yansa maza, ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka ɗaga, su zama rabonsu daga cikin hadayu na salama na Isra'ilawa. Ya ba Haruna, firist, da 'ya'yansa maza, su zama rabonsu har abada daga cikin hadayu na Isra'ilawa.

35. Wannan shi ne rabon da aka keɓe wa Haruna da 'ya'yansa maza, daga cikin hadayun da ake yi da wuta ga Ubangiji, tun a ranar da aka keɓe su firistoci na Ubangiji.

36. Ubangiji ya umarci Isra'ilawa su ba firistoci wannan a ranar da aka keɓe su. Wannan hakkinsu ne a dukan zamanansu.

37. Waɗannan su ne ka'idodin hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi, da hadaya don keɓewa, da hadaya ta salama.

38. Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a Dutsen Sina'i, can cikin hamada, a ranar da ya faɗa wa Isra'ilawa su kawo hadayunsu gare shi.

Karanta cikakken babi L. Fir 7