Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 7:14-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Daga cikin wannan zai miƙa waina ɗaya daga kowace hadaya don hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist wanda ya yayyafa jinin hadaya ta salama.

15. Za a ci naman hadayarsa ta salama da aka miƙa don godiya a ranar da aka miƙa ta. Kada a bar naman ya kai safe.

16. Amma idan hadayarsa ta cika wa'adi ce, ko ta yardar rai ce, sai a ci ta a ranar da aka miƙa ta, kashegari kuma a ci abin da ya ragu.

17. Amma idan ba a cinye naman hadayar ba har ya kai kwana uku, kada a ci, sai a ƙone shi da wuta.

18. Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami fa'idar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci ya yi laifi.

19. Kada a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki, sai a ƙone shi da wuta.Duk wanda yake da tsarki zai iya cin nama.

20. Amma wanda ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji lokacin da ba shi da tsarki, za a raba shi da mutenensa.

21. Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa.

22. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

23. ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, kada su ci kitsen sa, ko na tunkiya, ko na akuya.

24. Kitsen dabbar da ta mutu mushe, da kitsen dabbar da namomin jeji suka yayyaga, za a iya yin wani amfani da shi, amma kada a kuskura a ci.

25. Duk mutumin da ya ci kitsen dabbar da aka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, za a raba shi da mutanensa.

26. Ko kaɗan, ba za a yi abinci da jini ba, ko na tsuntsu, ko na dabba, a inda suke duka.

27. Duk mutumin da ya karya wannan doka za a raba shi da mutanensa.

28. Ubangiji kuma ya ba Musa waɗannan ka'idodi

29. don mutanen Isra'ila, cewa, wanda zai miƙa hadayarsa ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama.

30. Sai shi kansa ya kawo hadayar da za a ƙona. Zai kawo kitsen da ƙirjin. Za a yi hadaya ta kaɗawa da ƙirjin a gaban Ubangiji.

31. Firist zai ƙone kitsen a bisa bagaden, amma ƙirjin zai zama rabon Haruna da 'ya'yansa maza.

Karanta cikakken babi L. Fir 7