Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 4:27-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. In wani daga cikin talakawa ya yi zunubi, ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.

28. Sa'ad da aka sanar da shi zunubin da ya aikata, sai ya kawo akuya marar lahani don yin hadaya saboda zunubinsa.

29. Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya don zunubi, ya yanka hadayar a wurin hadaya ta ƙonawa.

30. Firist zai ɗibi jinin da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sa'an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden.

31. Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.

32. Idan kuwa daga cikin 'yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo 'yar tunkiya marar lahani.

33. Zai ɗibiya hannunsa a kan kan abin yin hadaya don zunubin, sa'an nan ya yanka a wurin da akan yanka hadaya ta ƙonawa.

34. Sai firist ya ɗibi jinin abin yin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sauran jinin kuwa ya zuba a gindin bagaden.

35. Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi masa kafara saboda zunubin da ya aikata, za a kuwa gafarta masa.

Karanta cikakken babi L. Fir 4