Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 27:19-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Idan shi wanda ya keɓe gonar yana so ya fanshe ta, to, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin kuɗin gonar, gonar kuwa za ta zama tasa.

20. Amma idan ba ya so ya fanshi gonar, ko kuwa ya riga ya sayar wa wani da gonar, faufau, ba zai sāke fansarta ba.

21. Sa'ad da aka mayar da gonar a shekara ta hamsin ta murna, za ta zama tsattsarka ta ubangiji kamar gonar da aka keɓe. Firist ne zai mallaka ta.

22. Idan kuwa ya keɓe wa Ubangiji gonar da ya saya, wadda ba ta gādo ba,

23. sai firist ya kimanta tamaninta har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Shi mutumin zai ba da yawan abin da aka kimanta a ranar, abu mai tsarki ne ga Ubangiji.

24. A cikin shekara ta hamsin ta murna, sai a mayar da gonar ga wanda aka saye ta a hannunsa, wanda gonarsa ce ta gādo.

25. Sai a kimanta tamanin kowane abu bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

26. Kowane ɗan fari na dabba na Ubangiji ne, kada wani ya fanshi sa ko tunkiya, gama na Ubangiji ne.

27. Idan dabbar marar tsarki ce, sai mai ita ya kimanta tamanin kuɗinta, ya ƙara da humushin kuɗin, ya saya. Idan ba a fansa ba, sai a sayar bisa ga tamaninta.

28. Amma iyakar abin da mutum ya ba Ubangiji ɗungum daga cikin abubuwan da yake da su, ko mutum ko dabba, ko gonarsa ta gādo, ba za a sayar ko a fansar ba, gama kowane abu da aka keɓe mafi tsarki ne ga Ubangiji.

29. Ko da mutum ne aka ba Ubangiji ɗungum, ba za a fanshe shi ba, sai a kashe shi.

30. Dukan ushirin amfanin ƙasar, ko na hatsi ne, ko na 'ya'yan itatuwa ne, na Ubangiji ne, gama tsattsarka ne ga Ubangiji.

31. Idan wani yana so ya fanshi ushiri na kowane iri, sai ya ƙara humushin tamanin ushirin.

32. Dukan ushiri na shanu, da na tumaki da awaki, duk dai dabbar da ta zama ta goma bisa ga ƙirgar makiyayan, keɓaɓɓiya ce, ta Ubangiji ce.

33. Ba ruwan kowa da kyanta ko rashin kyanta. Kada kuma a musaya ta. Idan kuwa an musaya ta, sai dai su zama tsarkakakku ga Ubangiji, ita da abar da aka yi musayar. Ba za a fanshe su ba.

34. Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sinai saboda isra'ilawa.

Karanta cikakken babi L. Fir 27