Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 26:26-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma'auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba.

27. “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,

28. sai ni ma in tayar muku da fushi, in hukunta ku har riɓi bakwai, saboda zunubanku.

29. Za ku ci naman 'ya'yanku mata da na 'ya'yanku maza.

30. Zan lalatar da masujadanku, in rurrushe bagaden ƙona turarenku, in jefar da gawawwakinku a kan gumakanku, raina kuwa zai ji ƙyamarku.

31. Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.

32. Ni zan lalatar da ƙasar har maƙiyanku da suke zaune a ciki za su yi mamaki.

33. Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace.

34. Sa'an nan ƙasar za ta ji daɗin hutunta muddin tana zaune kango. Sa'ad da kuke a ƙasar maƙiyanku, ƙasar za ta huta, taji daɗin hutunta.

35. Muddin tana zaune kufai za ta sami hutawa, hutawa asabatan da ba ta samu ba a lokacin da kuke zaune cikinta.

36. “Amma ga waɗanda suka ragu, zan sa fargaba a zuciyarsu sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu. Ko motsin ganye kawai ma zai razanar da su su sheƙa a guje kamar waɗanda ake fafara da takobi, ga shi kuwa, ba mai korarsu, za su kuwa fāɗi.

37. Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake ba wanda yake korarsu. Ba za su sami ikon tsaya wa maƙiyansu ba.

38. Za ku mutu a cikin al'ummai. Ƙasar maƙiyanku za ta haɗiye ku.

Karanta cikakken babi L. Fir 26