Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 25:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Shekara shida za su yi, suna ta noman gonakinsu, suna kuma ta aske gonakin inabinsu, suna tattara amfaninsu.

4. Amma shekara ta bakwai ta Ubangiji ce, sh ekara ce ta hutawa ga ƙasar. Kada su nomi gonakinsu, ko kuwa su aske inabinsu.

5. Kada su girbe gyauron gonakinsu da na inabin da ba su yi wa aski ba. Za ta zama shekarar hutawa ta musamman ga ƙasar.

6. A shekarar nan ɗin ƙasar za ta tanada musu abinci, da su da bayinsu mata, da maza, da barorinsu na ijara, da baƙon da yake zaune tare da su,

7. har da dabbobinsu na gida da na jeji. Duk albarkar da ƙasar za ta bayar, za ta zama abinci.

8. Sai su ƙidaya shekara bakwai har sau bakwai. Shekarar nan bakwai sau bakwai su ne shekara arba'in da tara a gare su.

9. A ranar kafara, goma ga wata na bakwai za su busa ƙahon rago da ƙarfi cikin ƙasarsu duka.

10. Shekara ta hamsin kuwa za su keɓe ta, su yi shelar 'yanci cikin ƙasar duka ga dukan mazaunanta. Za ta zama shekarar murna a gare su. Kowa zai koma mahallinsa, ko wannensu kuma wurin danginsa.

11. Shekarar nan ta hamsin za ta zama shekara ta murna a gare su. A cikinta ba za su yi shuka, ko su girbe gyauro ba, ba kuwa za su tattara 'ya'yan inabin da ba su yi wa aski ba.

12. Shekara ce ta murna, za ta zama keɓaɓɓiya a gare su. Za su ci albarkar da gonakin suka bayar.

13. Ubangiji ya ce, “A wannan shekara ta hamsin ta murna kowa zai koma mahallinsa.

14. In ka sayar, ko ka sayi gona a wurin ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, kada ku cuci juna.

15. Idan za ka yi sayayya a wurin maƙwabcinka, sai ka lura da yawan shekarun da za ka mora kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo.

Karanta cikakken babi L. Fir 25