Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Tsarkin Firistoci

1. Ubangiji kuma ya umarce Musa, ya faɗa wa 'ya'yan Haruna, maza, firistoci cewa, “Kada ko wannensu ya ƙazantar da kansa ta wurin gawar mutanensa,

2. sai dai gawar iyalinsa na kurkusa, wato, gawar mahaifiyarsa, da ta mahaifinsa, da ta ɗansa, da ta 'yarsa, da ta ɗan'uwansa,

3. da ta 'yar'uwarsa, budurwa, da take kusa da shi, wadda ba ta yi aure ba tukuna. Saboda su ya iya ƙazantar da kansa.

4. Kada ya ƙazantar da kansa saboda dangantakar aure cikin mutanensa.

5. “Kada su aske kansu ƙwal, ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsaga jikinsu.

6. Sai su kasance da tsarki, kada su ƙasƙantar da sunana domin su ne masu kawo hadaya ta ci, masu ƙone hadayu da wuta gare ni, don haka sai su kasance da tsarki.

7. Kada firist ya auri karuwa, ko wadda mijinta ya sake ta, gama shi tsattsarka ne gare ni.

8. Dole jama'a su gan su da tsarki, gama suna miƙa hadaya ta ci gare ni. Ni ne Ubangiji, ni mai tsarki ne, na kuwa tsarkake mutanena.

9. 'Yar firist wadda ta ɓata kanta da yin aikin karuwanci, ta ƙasƙantar da mahaifinta, sai a ƙone ta da wuta.

10. “Firist wanda yake babba cikin 'yan'uwansa da aka zuba masa man keɓewa, aka kuma keɓe shi ya riƙa sa tufafin firist, kada ya bar gashin kansa buzu-buzu, ko kuwa ya kyakketa tufafinsa.

11. Kada ya kusaci gawa, ko gawar mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa don kada ya ƙazantu.

12. An keɓe shi domina, kada ya ƙazantar da kansa, kada kuwa ya ɓata alfarwa ta sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce.

13. Sai ya auri budurwa.

14. Kada ya auri mace wadda mijinta ya rasu, ko sakakkiya, ko karuwa, amma ya auri budurwa daga cikin kabilarsa,

15. domin kada ya ƙazantar da 'ya'yansa waɗanda ya kamata su zama tsarkakakku. Ni ne Ubangiji, na kuwa keɓe shi ya zama babban firist.”

16. Sai Ubangiji ya umarce Musa

17. ya faɗa wa Haruna cewa, “Kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani ya kusato garin ya miƙa hadaya ta ci gare ni har abada.

18. Duk mutumin da yake da lahani na makanta, ko gurguntaka, ko rauni a fuska, ko gaɓar da ta fi wata,

19. ko tauyayye a ƙafa ko a hannu,

20. ko mai ƙusumbi, ko wada, ko mai lahani a ido, ko cuta mai sa ƙaiƙayi, ko kirci, ko dandaƙaƙƙe, ba zai kusato garin ya miƙa hadaya ba.

21. Duk mutumin da yake cikin zuriyar Haruna firist, wanda yake da lahani, ba zai kusato garin ya miƙa hadaya ta ci gare ni ba.

22. Amma zai iya ci daga cikin tsattsarkan abincin da aka miƙa mini, da abinci mafi tsarki.

23. Sai dai ba zai kusaci labulen, ko ya tafi kusa da bagaden ba, domin yana da lahani, don kada ya ɓata wuraren yin sujada, gama ni ne Ubangiji, ni kuwa na tsarkake su.”

24. Haka nan kuwa Musa ya faɗa wa Haruna, da 'ya'yan Haruna, maza, da dukan Isra'ilawa.