Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 20:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. In kuma mace ta yi ƙoƙari har ta kwana da dabba, sai a kashe matar tare da dabbar, alhakin jininsu yana wuyansu.

17. “Idan mutum ya auri ƙanwarsa ko kuma 'yar mahaifinsa, sai a ƙasƙantar da su a bainar jama'a, a kuwa kore su daga cikin jama'a. Ya kwana da ƙanwarsa ke nan, tilas su sha hukuncin laifinsu.

18. Idan mutum ya kwana da mace a lokacin hailarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama'arsu, gama sun karya ka'idodi a kan rashi tsarki.

19. “Idan mutum ya kwana da bābarsa ko innarsa, za a hukunta duka biyunsu saboda abin ƙyama da suka yi.

20. Idan kuma mutum ya kwana da matar kawunsa, ya ƙasƙantar da kawunsa, sai su ɗauki alhakin laifinsu, za su mutu ba haihuwa.

21. Idan mutum ya auri matar ɗan'uwansa, ya yi mugun abu, za su mutu ba haihuwa, gama ya ƙasƙantar da ɗan'uwansa.

22. “Sai fa ku kiyaye dokokina duka, da ka'idodina duka, ku kuma aikata su domin kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku.

23. Kada ku bi al'adun waɗannan al'ummai, waɗanda nake kora a gabanku, gama sun aikata waɗannan al'amura, don haka nake ƙyamarsu.

24. Amma ni na faɗa muku, za ku gāji ƙasarsu, zan kuwa ba ku ita, ku mallake ta, ƙasar da take da yalwar abinci. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga sauran al'ummai.

25. Domin haka sai ku bambanta tsakanin halattattun dabbobi da haramtattun dabbobi, da tsakanin haramtattun tsuntsaye da halattattun tsuntsaye. Kada ku ƙazantar da kanku da haramtattun dabbobi, ko da tsuntsaye, ko da kowane abu mai rarrafe bisa ƙasa, waɗanda na ware su, su zama haramtattu a gare ku.

26. Sai ku zama tsarkakakku a gare ni, gama ni Ubangiji Mai Tsarki ne, na kuwa keɓe ku daga sauran al'umman duniya don ku zama nawa.

27. “Namiji ko macen da yake da mabiya ko maita, sai a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu, alhakin jininsu yana kansu.”

Karanta cikakken babi L. Fir 20