Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 19:33-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. “Idan baƙo ya baƙunce ku a ƙasarku, kada ku cuce shi.

34. Amma ku ɗauke shi tankar ɗan ƙasa, ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.

35. “Kada ku cuci wani wajen yin amfani da kowane irin ma'auni na ƙarya, wato, awon tsawo, ko na nauyi, ko na ruwa.

36. Sai ma'auninku na awon nauyi, da mudun awo, da mudun awon abin da yake ruwa ruwa, su zama na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar.

37. Sai ku kiyaye, ku aikata dokokina da umarnaina duka. Ni ne Ubangiji.”

Karanta cikakken babi L. Fir 19