Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 18:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ubangiji ya ba da waɗannan ka'idodi kuma. Kada kowane mutum ya kusaci 'yar'uwarsa don ya kwana da ita. Ya ce, “Ni ne Ubangiji.”

7. Kada ya ƙasƙantar da mahaifinsa, wato, kada ya kwana da mahaifiyarsa, kada ya ƙasƙantar da mahaifiyarsa.

8. Kada ya kwana da matar mahaifinsa, gama ita matar mahaifinsa ce.

9. Kada ya kwana da 'yar'uwarsa, 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa, ko a gida ɗaya aka haife ta da shi, ko a wani gida dabam.

10. Kada ya kwana da jikanyarsa gama zai zama ƙasƙanci a gare shi.

11. Kada ya kwana da 'yar matar mahaifinsa, wadda mahaifinsa ya haifa, tun da yake ita 'yar'uwarsa ce.

12. Kada ya kwana da bābarsa gama 'yar'uwar mahaifinsa ce.

13. Kada ya kwana da innarsa, gama ita 'yar'uwar mahaifiyarsa ce.

14. Kada ya kwana da matar ɗan'uwan mahaifinsa, gama ita ma bābarsa ce.

15. Kada ya kwana da matar ɗansa, gama ita surukarsa ce.

Karanta cikakken babi L. Fir 18