Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 18:25-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Har ƙasar ma ta ƙazantu, don haka Ubangiji ya hukunta muguntarta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta.

26. Amma su sai su kiyaye dokokin Ubangiji da ka'idodinsa. Kada su aikata ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa na banƙyama, ko haifaffe na gida, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu.

27. Gama mazaunan ƙasar da suka riga su, sun aikata dukan abubuwa masu banƙyaman nan, don haka ƙasar ta ƙazantu.

28. Kada kuma ƙasar ta amayar da su idan sun ƙazantar da ita, kamar yadda ta amayar da al'ummar da ta riga su zama a cikinta.

29. Duk wanda ya aikata abu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa masu banƙyaman nan za a raba shi da jama'a.

30. Ubangiji kuma ya ce, “Don haka sai ku kiyaye umarnina, kada ku kiyaye dokoki na banƙyama waɗanda aka kiyaye kafin ku zo, kada ku ƙazantu da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

Karanta cikakken babi L. Fir 18