Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 18:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya ce wa Musa

2. ya faɗa wa mutanen Isra'ila cewa, “Ni ne Ubangiji Allahnku.

3. Kada ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan'ana inda nake kai ku. Kada ku kiyaye dokokinsu.

4. Amma ku bi ka'idodina, ku yi tafiya a cikinsu, gama ni ne Ubangiji Allahnku.

5. Domin haka sai ku kiyaye dokokina da ka'idodina waɗanda ta wurin kiyaye su mutum zai rayu. Ni ne Ubangiji.”

6. Ubangiji ya ba da waɗannan ka'idodi kuma. Kada kowane mutum ya kusaci 'yar'uwarsa don ya kwana da ita. Ya ce, “Ni ne Ubangiji.”

7. Kada ya ƙasƙantar da mahaifinsa, wato, kada ya kwana da mahaifiyarsa, kada ya ƙasƙantar da mahaifiyarsa.

8. Kada ya kwana da matar mahaifinsa, gama ita matar mahaifinsa ce.

9. Kada ya kwana da 'yar'uwarsa, 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa, ko a gida ɗaya aka haife ta da shi, ko a wani gida dabam.

10. Kada ya kwana da jikanyarsa gama zai zama ƙasƙanci a gare shi.

11. Kada ya kwana da 'yar matar mahaifinsa, wadda mahaifinsa ya haifa, tun da yake ita 'yar'uwarsa ce.

12. Kada ya kwana da bābarsa gama 'yar'uwar mahaifinsa ce.

13. Kada ya kwana da innarsa, gama ita 'yar'uwar mahaifiyarsa ce.

Karanta cikakken babi L. Fir 18