Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 14:43-55 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. Idan cutar ta sāke ɓulla a cikin gidan bayan da aka ciccire duwatsun, aka kuma kankare gidan, aka yi masa shafe,

44. sai firist ya je ya duba, idan cutar ya yaɗu a gidan, to, muguwar kuturta ce, gidan marar tsarki ne.

45. Sai a rushe gidan, a kwashe duwatsun gidan, da katakansa, da shafensa duka a zubar bayan birni a wuri marar tsarki.

46. Duk wanda ya shiga gidan bayan da an rufe shi, zai ƙazantu har maraice.

47. Wanda kuma ya kwana cikin gidan, sai ya wanke tufafinsa, haka kuma wanda ya ci abinci cikin gidan, zai wanke tufafinsa.

48. Amma idan firist ɗin ya zo, ya dudduba, ya ga tabon bai yaɗu a gidan ba, bayan da an yi wa gidan shafe, sai firist ya hurta, cewa, gidan tsattsarka ne domin tabon ya warke.

49. Don tsarkakewar gidan, sai maigida ya kawo 'yan tsuntsaye biyu, da itacen al'ul, da jan alharini, da ɗaɗɗoya.

50. Sai a yanka tsuntsu ɗaya a kasko cike da ruwa mai gudu.

51. Zai ɗauki itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini, da ɗayan tsuntsu mai ran, ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka a ruwan kaskon, ya yayyafa wa gidan sau bakwai.

52. Da haka zai tsarkake gidan da jini tsuntsun, da ruwa mai gudu, da tsuntsu mai ran, da itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da jan alharini.

53. Sa'an nan ya saki tsuntsu mai ran daga birni ya tafi saura. Ta haka zai yi kafara domin gidan, gidan kuwa zai tsarkaka.

54. Waɗannan su ne dokoki a kan cuce-cucen da akan ɗauka, da

55. kuturta a tufafi ko a jikin gida,

Karanta cikakken babi L. Fir 14