Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 14:34-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. “Sa'ad da kuka shiga ƙasar Kan'ana wadda nake ba ku ku mallaka, zan sa kuturta ta yaɗu a gidajenku.” Sa'an nan Ubangiji ya ba su waɗannan ka'idodi.

35. Mutumin da ya ga kuturta a gidansa, tilas ya je ya faɗa wa firist.

36. Firist kuwa ya umarta a fitar da dukan abin da yake cikin gidan kafin ya tafi ya dudduba tabo, domin kada kome da yake cikin gidan ya ƙazantu. Bayan haka sai firist ya shiga, ya duba gidan.

37. Zai dudduba tabon, idan akwai alamar tabon a bangayen gida kore-kore, ko jaja-jaja, idan an ga tabon ya yi zurfi cikin bangon,

38. sai firist ɗin ya fita daga cikin gidan zuwa ƙofa, ya rufe gidan har kwana bakwai.

39. A kan rana ta bakwai, sai firist ɗin ya komo, ya duba. Idan tabon ya yaɗu a jikin bangayen gidan,

40. sai ya umarta a ciccire duwatsun da suke da cutar, a zuba a wuri marar tsarki can bayan birnin,

41. ya sa a kankare jikin gidan duka. Shafen da suka kankare kuwa, sai su zubar da shi a wuri marar tsarki can bayan birnin.

42. Sa'an nan sai su kwaso waɗansu duwatsu, su sa su a wuraren da suka ciccire waɗancan. Sai a kawo laka a shafe gidan.

43. Idan cutar ta sāke ɓulla a cikin gidan bayan da aka ciccire duwatsun, aka kuma kankare gidan, aka yi masa shafe,

44. sai firist ya je ya duba, idan cutar ya yaɗu a gidan, to, muguwar kuturta ce, gidan marar tsarki ne.

45. Sai a rushe gidan, a kwashe duwatsun gidan, da katakansa, da shafensa duka a zubar bayan birni a wuri marar tsarki.

46. Duk wanda ya shiga gidan bayan da an rufe shi, zai ƙazantu har maraice.

Karanta cikakken babi L. Fir 14