Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 14:23-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. A rana ta takwas zai kawo su wurin firist don tsarkakewarsa a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji.

24. Sai firist ya ɗauki ɗan rago da man zaitun, ya miƙa su hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.

25. Sa'an nan ya yanka ɗan ragon don laifi, ya ɗibi jinin hadaya don laifin, ya shafa a leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da a babban yatsan hannunsa na dama, da ƙafarsa ta dama.

26. Firist ɗin kuma zai ɗibi man ya zuba cikin tafin hannunsa na hagu.

27. Sai ya yayyafa man da yake cikin tafin hannunsa na hagu sau bakwai a gaban Ubangiji da yatsansa na hannun dama.

28. Ya kuma shafa man da ya ragu cikin hannunsa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da a babban yatsan hannun damansa, da kuma a babban yatsan ƙafar damansa, a inda aka shafa jinin hadaya don laifin.

29. Sauran man da yake cikin tafin hannunsa zai zuba a bisa wanda ake tsarkakewar, ya yi kafara dominsa a gaban Ubangiji.

30. Sai mutumin ya ba da kurciyoyi, ko 'yan tattabarai yadda ya iya,

31. ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa tare da hadaya ta gari. Firist ɗin kuma zai yi kafara a gaban Ubangiji domin wanda ake tsarkakewar.

32. Wannan ita ce doka a kan mai ciwon kuturta wanda ba shi da isasshen abin bayarwa don yin hadayun tsarkakewarsa.

33. Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

34. “Sa'ad da kuka shiga ƙasar Kan'ana wadda nake ba ku ku mallaka, zan sa kuturta ta yaɗu a gidajenku.” Sa'an nan Ubangiji ya ba su waɗannan ka'idodi.

35. Mutumin da ya ga kuturta a gidansa, tilas ya je ya faɗa wa firist.

36. Firist kuwa ya umarta a fitar da dukan abin da yake cikin gidan kafin ya tafi ya dudduba tabo, domin kada kome da yake cikin gidan ya ƙazantu. Bayan haka sai firist ya shiga, ya duba gidan.

Karanta cikakken babi L. Fir 14