Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 14:21-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Amma idan matalauci ne, har ba zai iya samun waɗannan abubuwa ba, sai ya kawo ɗan rago ɗaya domin hadaya don laifi, a yi hadaya ta kaɗawa, a yi kafara dominsa. Ya kuma kawo humushin garwa na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun don yin hadaya ta gari, da rabin moɗa na mai,

22. da kuma kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu yadda dai ya iya. Ɗayan domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa.

23. A rana ta takwas zai kawo su wurin firist don tsarkakewarsa a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji.

24. Sai firist ya ɗauki ɗan rago da man zaitun, ya miƙa su hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.

25. Sa'an nan ya yanka ɗan ragon don laifi, ya ɗibi jinin hadaya don laifin, ya shafa a leɓatun kunnen dama na mutumin da za a tsarkake, da a babban yatsan hannunsa na dama, da ƙafarsa ta dama.

26. Firist ɗin kuma zai ɗibi man ya zuba cikin tafin hannunsa na hagu.

27. Sai ya yayyafa man da yake cikin tafin hannunsa na hagu sau bakwai a gaban Ubangiji da yatsansa na hannun dama.

28. Ya kuma shafa man da ya ragu cikin hannunsa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsarkake, da a babban yatsan hannun damansa, da kuma a babban yatsan ƙafar damansa, a inda aka shafa jinin hadaya don laifin.

29. Sauran man da yake cikin tafin hannunsa zai zuba a bisa wanda ake tsarkakewar, ya yi kafara dominsa a gaban Ubangiji.

30. Sai mutumin ya ba da kurciyoyi, ko 'yan tattabarai yadda ya iya,

31. ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa tare da hadaya ta gari. Firist ɗin kuma zai yi kafara a gaban Ubangiji domin wanda ake tsarkakewar.

Karanta cikakken babi L. Fir 14