Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 9:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Hikima za ta ƙara shekarunka.

12. Kai ne da riba in ka sami hikima. Kai za ka sha hasara in ka ƙi ta.

13. Wawanci kamar mace ce mai kwakwazo, jahila, marar kunya.

14. Takan zauna a ƙofar gidanta, ko a wurin da ya fi duka bisa a cikin gari.

15. Takan yi ta kiran masu wucewa waɗanda hankalinsu yake a kan ayyukansu, ta ce,

16. “Ku shigo, ku jahilai!” Takan ce wa dolo,

17. “Ruwan da aka sata ya fi daɗi, haka nan kuma abincin da ake satar ya fi daɗi.”

18. Waɗanda suka fāɗa a hannunta ba su sani mutuwa za su yi ba, waɗanda suka riga sun shiga kuwa suna can sun nutse cikin lahira.

Karanta cikakken babi K. Mag 9